Rashford ya tsawaita zamansa a United

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rashford ya ci wa Manchester United kwallaye takwas a wasanni 18.

Matashin dan kwallon Manchester United, Marcus Rashford, ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a kungiyar zuwa watan Yunin 2020.

Kwallaye biyu ya ci wa United a ranar farko da ya fara buga mata wasa a karawar da suka yi da FC Midtjyland da kuma wadda ya zura a gasar Premier kwanaki uku tsakani.

Rashford ya ci wa Manchester United kwallaye takwas a wasanni 18 tun daga lokacin da ya buga.

Dan kwallon yana cikin 'yan wasa 26 na kwarya-kwarya da Ingila ta sanar, kafin ta fitar da sunayen 23 da za su wakilce ta a gasar cin kofin nahiyar Turai a ranar Talata.

Haka kuma United din ta kulla sabuwar yarjejeniya da dan kwallon Kamaru, Borthwick-Jackson zuwa shekarar 2020, domin ya ci gaba da murza-leda a Old Trafford.