An kama ɗan wasan Ivory Coast Aurier

Hakkin mallakar hoto
Image caption An taba dakatar da Aurier saboda ya zargi koci.

An kama ɗan wasan kwallon kafar Ivory Coast Serge Aurier a birnin Paris bayan ya ci zarafin wani ɗan sanda a wajen dabdala.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce ɗan wasan ya yi wa ɗan sandan gula a maƙogwaro.

A watan Fabrairu ma, Paris St Germain, inda yake murza leda, ya dakatar da Aurier, bayan ya zagi koci da wasu 'yan wasan kulob ɗin.