Bellerin na cikin tawagar Spaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An zabi Hector Bellerin cikin tawagar kwallon Spaniya

An sanya dan wasan baya na Arsenal Hector Bellerin a cikin tawagar kwallon Spaniya, a wasan da za su yi na neman cin kofin Euro 2016.

Bellarin ya shiga jerin sunayen 'yan wasan da za su yi wasan ne bayan da Dani Carvajal ya ji rauni a cinya, lokacin da kulob din Real Madrid ya fafata da Atletico Madrid a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Bellerin, mai shekara 21, ya ci kwallonsa ta farko a wasan da suka fafata da Bosnia da Herzegovina ranar Lahadi da daddare.

Zuwa yanzu Spaniya ta ambaci sunayen 'yan wasa 19, kuma ana sa rana za ta ambaci ragowar hudun a ranar Talata da yamma.

Shi ma dan wasan Manchester United David de Gea, da na Manchester City, David Silva na cikin tawagar kwallon Spaniyan.