Euro 2016: Kompany zai yi wa BBC sharhi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Vincent Kompany ya ce bai ji dadin rashin wakiltar Belgium ba.

Dan Manchester City da Belgium Vincent Kompany zai shiga jerin masu yi wa BBC sharhi a gasar Euro 2016.

Kompany, wanda ya zura kwallaye 70, ba ya cikin 'yan wasan da za su buga gasar sakamakon raunin da ya ji a cinyarsa amma zai rika yin sharhi kan wasan daga dakin watsa labarai na Paris.

Dan wasan mai shekara 30 zai shiga cikin jerin masu yi wa BBC sharhi irin su Gary Lineker, Alan Shearer, Rio Ferdinand, Thierry Henry da Gianluca Vialli.

Kompany ya ce, "ban ji dadin rashin bin tawagar Belgium zuwa Faransa ba, amma duk da haka na ji dadi kasancewa mai yi wa BBC sharhi kan gasara."

Sauran mutanen da za su yi wa BBC sharhi Martin Keown, Jermaine Jenas, Danny Murphy, Robbie Savage, John Hartson, Dean Saunders, Chris Brunt, Neil Lennon, Gerry Armstrong, Mark Lawrenson, Kevin Kilbane da Jens Lehmann.