Jadawalin 'yan wasan da za su buga Euro 2016 (1)

Kungiyoyi 24 da za su fafata a gasar cin kofin Turai, wato Euro 2016, sun mikawa Faransa, mai masaukin baki, sunayen 'yan wasa 23 da za su wakilci kowacce kasa.

Sashen wasanni na BBC ya samu sunayen dukkan 'yan wasan da aka bayyana sunayensu cikin wadanda za su fafata, kamar haka:

Hakkin mallakar hoto Getty

Jamhuriyar Czech

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tomas Rosicky ya buga wa Arsenal wasa sau daya a kakar wasa ta bana a watan Janairu.

Tomas Rosicky, wanda ya buga wa Arsenal kwallon minti 19 kacal a kakar wasa ta bana saboda raunin da ya ji, ya murmure, kuma zai shiga gasar ta Euro 2016. Dan wasan na tsakiya zai so ya nuna bajintarsa ganin cewa zai bar Arsenal a lokacin bazara idan wa'adinsa ya kare.

Masu tsaron raga: Petr Cech (Arsenal), Tomas Vaclik (Basel), Tomas Koubek (Sparta Prague)

Masu tsaron gida: Theodor Gebre Selassie (Werder Bremen), Pavel Kaderabek (Hoffenheim), David Limbersky (Viktoria Pilsen), Marek Suchy (Basel), Michal Kadlec (Sparta Prague), Tomas Sivok (Bursaspor), Roman Hubnik (Viktoria Pilsen), Daniel Pudil (Sheffield Wednesday)

'Yan wasan tsakiya: Borek Dockal (Sparta Prague), Jiri Skalak (Brighton), Vladimir Darida (Hertha Berlin), Daniel Kolar (Viktoria Pilsen), Ladislav Krejci (Sparta Prague), Josef Sural (Sparta Prague), David Pavelka (Kasimpasa), Jaroslav Plasil (Bordeaux), Tomas Rosicky (Arsenal)

'Yan wasan gaba: Milan Skoda (Slavia Prague), Tomas Necid (Bursaspor), David Lafata (Sparta Prague).

Ingila

Image caption Tsohon dan wasan Manchester City da Tottenham Vedran Corluka ya buga wa Croatia wasa sau 87.

Dan wasan Manchester United mai shekara 18 Marcus Rashford, wanda ya zura kwallo a fitowarsa ta farko, na cikin 'yan wasa 23 da koci Roy Hodgson ya zaba. Sai dai dan wasan Leicester City Danny Drinkwater ba ya cikin tawagar ta Ingila.

Masu tsaron raga: Joe Hart (Manchester City), Fraser Forster (Southampton), Tom Heaton (Burnley).

Masu tsaron gida: Gary Cahill (Chelsea), Chris Smalling (Manchester United), John Stones (Everton), Kyle Walker (Tottenham Hotspur), Ryan Bertrand (Southampton), Danny Rose (Tottenham Hotspur), Nathaniel Clyne (Liverpool).

'Yan wasan tsakiya: Dele Alli (Tottenham Hotspur), Ross Barkley (Everton), Eric Dier (Tottenham Hotspur), Jordan Henderson (Liverpool), Adam Lallana (Liverpool), James Milner (Liverpool), Raheem Sterling (Manchester City), Jack Wilshere (Arsenal).

'Yan wasan gaba: Wayne Rooney (Manchester United), Harry Kane (Tottenham Hotspur), Jamie Vardy (Leicester City), Daniel Sturridge (Liverpool), Marcus Rashford (Manchester United).

Faransa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dimitri Payet ne ya fi ci wa West Ham a kakar wasa ta bana, inda ya zura kwallaye 12.

Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema ba ya cikin wadanda za su murza wa Faransa leda. Sai dai dan wasan West Ham Dimitri Payet da takwaransa na Leicester N'golo Kante na cikin 'yan wasa 23 da za su wakilci kasar.

Masu tsaron raga: Benoit Costil (Rennes), Hugo Lloris (Tottenham Hotspur), Steve Mandanda (Marseille).

Masu tsaron gida: Lucas Digne (Roma), Patrice Evra (Juventus), Christophe Jallet (Lyon), Laurent Koscielny (Arsenal), Eliaquim Mangala (Manchester City), Samuel Umtiti (Lyon), Bacary Sagna (Manchester City), Adil Rami (Sevilla).

'Yan wasan tsakiya: Yohan Cabaye (Crystal Palace), Lassana Diarra (Marseille), N'Golo Kante (Leicester City), Blaise Matuidi (Paris St-Germain), Paul Pogba (Juventus), Moussa Sissoko (Newcastle United).

'Yan wasan gaba: Kingsley Coman (Bayern Munich), Andre-Pierre Gignac (Tigres), Olivier Giroud (Arsenal), Antoine Griezmann (Atletico Madrid), Anthony Martial (Manchester United), Dimitri Payet (West Ham United).

Jamus

Image caption Reus, mai shekara 27, bai buga gasar cin kofin duniya ta 2014, kuma an rika fargaba game da koshin lafiyarsa a kwanan baya.

An cire dan wasan gefe Marco Reus daga cikin ayarin da zai wakilci Jamus a gasar ta Euro 2016 saboda fargabar da ake yi game da koshin lafiyarsa.

Masu tsaron raga: Manuel Neuer (Bayern Munich), Bernd Leno (Bayer Leverkusen), Marc-Andre ter Stegen (Barcelona)

Masu tsaron gida: Jerome Boateng (Bayern Munich), Emre Can (Liverpool), Jonas Hector (Cologne), Benedikt Howedes (Schalke 04), Mats Hummels (Borussia Dortmund), Shkodran Mustafi (Valencia), Antonio Ruediger (Roma)

'Yan wasan tsakiya: Julian Draxler (VfL Wolfsburg), Sami Khedira (Juventus), Joshua Kimmich (Bayern Munich), Toni Kroos (Real Madrid), Thomas Muller (Bayern Munich), Mesut Ozil (Arsenal), Lukas Podolski (Galatasaray), Andre Schurrle (VfL Wolfsburg), Bastian Schweinsteiger (Manchester United), Julian Weigl (Borussia Dortmund)

'Yan wasan gaba: Mario Gomez (Besiktas), Mario Gotze (Bayern Munich), Leroy Sane (Schalke 04).

Hungary

Tsohon dan wasan West Brom da Fulham Zoltan Gera na cikin 'yan wasan da za su wakilci Hungary.

Masu tsaron raga: Gabor Kiraly (Haladas), Denes Dibusz (Ferencvaros), Peter Gulacsi (Leipzig)

Masu tsaron gida: Attila Fiola (Puskas Academy), Barnabas Bese (MTK Budapest), Richard Guzmics (Wisla Krakow), Roland Juhasz (Videoton), Adam Lang (Videoton), Tamas Kadar (Lech Poznan), Mihaly Korhut (Debrecen).

'Yan wasan tsakiya: Adam Pinter (Ferencvaros), Gergo Lovrencsics (Lech Poznan), Akos Elek (Diosgyor), Zoltan Gera (Ferencvaros), Adam Nagy (Ferencvaros), Laszlo Kleinheisler (Werden Bremen), Zoltan Stieber (Hamburg).

'Yan wasan gaba: Balazs Dzsudzsak (Bursaspor), Adam Szalai (Hoffenheim), Krisztian Nemeth (Al Gharafa), Nemanja Nikolics (Legia Warsaw), Tamas Priskin (Slovan Bratislava), Daniel Bode (ferencvaros).

Iceland

Iceland ta sanya tsohon dan wasan Chelsea Eidur Gudjohnsen cikin 'yan wasa 23 da za su fafata mata. Gudjohnsen ne dan wasan da ya fi zura wa kasar kwallo, inda ya ci kwallaye 25.

Masu tsaron raga: Hannes Halldorsson (Bodo/Glimt), Ogmundur Kristinsson (Hammarby), Ingvar Jonsson (Sandefjord).

Masu tsaron gida: Ari Skulason (OB), Hordur Magnússon (Juventus), Hjortur Hermannsson (PSV Eindhoven), Ragnar Sigurdsson (Krasnodar), Kari Arnason (Malmo), Sverrir Ingi Ingason (Lokeren), Birkir Saevarsson (Hammarby), Haukur Heidar Hauksson (AIK).

'Yan wasan tsakiya: Emil Hallfredsson (Udinese), Gylfi Sigurdsson (Swansea), Aron Gunnarsson (Cardiff), Theodor Elmar Bjarnason (AGF), Arnor Ingvi Traustason (Norrkoping), Birkir Bjarnason (Basel), Johann Gudmundsson (Charlton), Runar Mar Sigurjonsson (Sundsvall).

'Yan wasan gaba: Kolbeinn Sigthorsson (Nantes), Alfred Finnbogason (Augsburg), Jon Dadi Bodvarsson (Kaiserslautern), Eidur Gudjohnsen (molde).

Italiya

Italiya ta sanya 'yan wasa uku da ke buga gasar Premier a cikin ayarinta - 'yan wasan su ne Angelo Ogbonna na West Ham, da Matteo Darmian na Manchester United da kuma Graziano Pelle na Southampton.

Masu tsaron raga: Gianluigi Buffon (Juventus), Federico Marchetti (Lazio), Salvatore Sirigu (Paris St-Germain)

Masu tsaron gida: Andrea Barzagli (Juventus), Leonardo Bonucci (Juventus), Giorgio Chiellini (Juventus), Angelo Ogbonna (West Ham)

'Yan wasan tsakiya: Federico Bernardeschi (Fiorentina), Antonio Candreva (Lazio), Matteo Darmian (Manchester United), Daniele de Rossi (Roma), Mattia de Sciglio (Milan), Stephan El Shaarawy (Roma), Alessandro Florenzi (Roma), Emanuele Giaccherini (Bologna), Thiago Motta (Paris St-Germain), Marco Parolo (Lazio), Stefano Sturaro (Juventus)

'Yan wasan gaba: Eder (Sampdoria), Ciro Immobile (Torino), Lorenzo Insigne (Napoli), Graziano Pelle (Southampton), Simone Zaza (Juventus).

Northern Ireland

Will Grigg na cikin tawagar Northern Ireland bayan ya zura kwallaye 25 lokacin da kulob din Wigan ya lashe gasar League One.

Masu tsaron raga: Alan Mannus (St Johnstone), Michael McGovern (Hamilton Academical), Roy Carroll (Linfield)

Masu tsaron gida: Craig Cathcart (Watford), Jonathan Evans (West Bromwich Albion), Gareth McAuley (West Bromwich Albion), Luke McCullough (Doncaster Rovers), Conor McLaughlin (Fleetwood Town), Lee Hodson (MK Dons), Aaron Hughes (free agent), Patrick McNair (Manchester United), Chris Baird (Derby County)

'Yan wasan tsakiya: Steven Davis (Southampton), Oliver Norwood, (Reading), Corry Evans, (Blackburn Rovers), Shane Ferguson (Millwall), Stuart Dallas (Leeds United), Niall McGinn (Aberdeen), Jamie Ward (Nottingham Forest)

'Yan wasan gaba: Kyle Lafferty (Norwich City), Conor Washington (Queens Park Rangers), Josh Magennis (Kilmarnock), Will Grigg (Wigan Athletic).

Poland

Image caption Robert Lewandowski ya zura kwallaye 34 a wasanni 75 da ya bugawa Poland.

Dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski ne zai jagoranci tawagar Poland. Dan wasan ya zura kwallaye 13 a wasanni 10 da ya buga a lokacin da suke neman cancantar shiga gasar.

Masu tsaron raga: Lukasz Fabianski (Swansea City), Wojciech Szczesny (AS Roma), Artur Boruc (Bournemouth)

Masu tsaron gida: Thiago Cionek (Palermo), Kamil Glik (Torino), Artur Jedrzejczyk (FK Krasnodar), Michal Pazdan (Legia Warsaw), Lukasz Piszczek (Borussia Dortmund), Bartosz Salamon (Cagliari), Jakub Wawrzyniak (Lechia Gdansk)

'Yan wasan tsakiya: Jakub Blaszczykowski (Borussia Dortmund), Kamil Grosicki (Rennes), Tomasz Jodlowiec (Legia Warsaw), Bartosz Kapustka (Cracovia), Grzegorz Krychowiak (Sevilla), Karol Linetty (Lech Poznan), Krzysztof Maczynski (Wisla), Slawomir Peszko (Lechia Gdansk), Filip Starzynski (Zaglebie Lubin), Piotr Zielinski (Udinese)

'Yan wasan gaba: Arkadiusz Milik (Ajax), Robert Lewandowski (Bayern Munich), Mariusz Stepinski (Ruch Chorzow).

Portugal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cristiano Ronaldo ya wartsake bayan ya taimakawa Real Madrid wajen daukar kofin Zakarun Turai.

Cristiano Ronaldo ne zai ja ragamar tawagar Portugal inda yake sa ran kara zura kwallaye a kan 56 da ya zura a gasar kasashen duniya. Tsohon dan wasan Chelsea Ricardo Carvalho ma zai shiga jerin 'yan wasan, duk da yake bai je Euro 2012 da gasar cin kofin duniya ta 2014 ba.

Masu tsaron raga: Rui Patricio (Sporting), Anthony Lopes (Lyon), Eduardo (Dínamo Zagreb)

Masu tsaron gida: Vieirinha (Wolfsburg), Cedric (Southampton), Pepe (Real Madrid), Ricardo Carvalho (Monaco), Bruno Alves (Fenerbahce), Jose Fonte (Southampton), Eliseu (Benfica), Raphael Guerreiro (Lorient)

'Yan wasan tsakiya: Renato Sanches (Bayern Munich), Adrien Silva (Sporting), Andre Gomes (Valencia), Joao Mario (Sporting)

'Yan wasan gaba: Rafa Silva (Braga), Ricardo Quaresma (Besiktas), Nani (Fenerbahce), Cristiano Ronaldo (Real Madrid), Eder (Lille).