Serena ta fitar da Svitolina daga French Open

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Williams za ta buga wasan daf da na kusa da karshe ne tsakanin Carla Suarez Navarro da Yulia Putintseva.

Serena Williams ta kai wasan zagaye na biyar a gasar kwallon tennis ta French Open, bayan ta doke Elina Svitolina.

Williams, ‘yar kasar Amurka, ta samu nasara ne a kan Svitolina ta Ukraine da ci 6-1 6-1.

Za ta buga wasan daf da na kusa da karshe ne Carla Suarez Navarro ko kuma Yulia Putintseva.

Ita ma Timea Bacsinszky ta cinye Venus Williams da ci 6-2 6-4, yayin da Kiki Bertens ta doke Madison Keys da ci 7-6 (7-4) 6-3.