Djokovic ya kai zagayen gaba a French Open

Novak Djokovic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Novak Djokovic ya kan ganiyarsa a gasar Tennis

Novak Djokovic ya kai wasan daf da karshe a gasar French Open, bayan da ya doke Tomas Berdych.

Djokovic ya samu nasarar ne da ci 6-3 7-5 da kuma 6-3, zai kuma buga wasan daf da karshen ne da Dominic Thiem.

Thiem ya kai wasan daf da karshe ne a karon farko a Grand Slam, bayan da ci David Goffin 4-6 7-6 (9-7) 6-4 da kuma 6-1.

Djokovic na fatan lashe kofin na French Open a karon farko.