An kwantar da Muhammad Ali a asibiti

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana sa ran zai zai zauna na wani dan lokaci a asibiti.

An kwantar da fitaccen dan damben duniya Muhammad Ali a asibiti saboda yana fama da wata cuta da ta shafi numfashinsa.

Ali, mai shekaru 74, na samun kulawar likitoci a wani mataki na rigakafi, kuma an ce yana cikin "yanayi mai kyau".

Ana sa ran zai zai zauna na wani dan lokaci a asibiti.

Ali ya kamu da cutar Parkinson ne a shekarar 1984, bayan da ya yi ritaya daga dambe.

Rabon zakaran damben da asibiti tun watan Janairun 2015 bayan da ya kamu da wata cuta da ta shafi mafitsararsa.

Mai magana da yawun iyalinsa ya tabbatar da halin Ali, wanda ya lashe kambun dambe na duniya sau uku, yake ciki, sai dai bai bayyana asibitin da aka kwantar da shi ba.