Murray zai kara da Djokovic a French Open

Andy Murray Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rabon da dan Birtaniya ya lashe gasar tun 1936

Andy Murray ya kai zagayen karshe na gasar cin kofin Tennis ta French Open bayan da ya lallasa mai rike da kanbun Stan Wawrinka da ci 6-4 6-2 4-6 6-2.

Dan wasan, wanda ya fito daga yankin Scotland, ya zamo dan Birtaniya na farko da ya kai matakin karshe na gasar tun shekarar 1937.

A yanzu zai fafata a wasan karshe ne da zakaran wasan Tennis Novak Djokovic a ranar Lahadi.

Djokovic ya doke dan Austria Dominic Thiem da ci 6-2 6-1 6-4.

Murray, mai shekaru 29, yana fatan cimma nasarar da dan Birtaniya Fred Perry yayi, inda ya lashe gasar ta French Open a shekarar 1936.