Bissau za ta je Africa Cup 2017

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Guinea Bissau, Mario Vaz

Guinea Bissau ta samu gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka ta 2017, bayan da Kenya ta doke Congo Brazaville da ci 2-1, a wasan da suka kara ranar Lahadi.

Ita dai Bissau ta kara da Zambia ne ranar Asabar, a wasan neman cancantar zuwa gasar, a inda kuma aka tashi 3-2.

Nasarar da Kenya ta samu a kan Congo Brazaville ce dai ta ba wa Bissau din sa'a.

Wannan dai shi ne karon farko da Bissau za ta je gasar ta African Cup of Nations.

Ita ma Ghana ta cancanci zuwa gasar sakamakon lallasa Mauritius da ta yi da ci 2-0.