Duniya tana alhinin Muhammad Ali

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Muhammad Ali ya rayu tsawon shekaru 74

Tun bayan sanar da rasuwar fitaccen dan damben nan, Muhammad Ali, mutane daga fagen rayuwa daban-daban suka nuna alhininsu dangane da rasuwar.

Mafi yawancin mutanen sun bayyana alhinin nasu ta kafar sada zumunta ta Twitter.

Shugabannin duniya:

Obama: Ali ya girgiza duniya, Allah ya jikan ka Muhammad Ali.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Amurka, Barack Obama

David Cameron: Muhammad Ali ba zakaran wasan dambe ba ne kawai, zakaran nemawa mutane hakkinsu ne kuma ya zamo abin koyi ga kowa.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firaiministan Ingila, David Cameron.
Mawaka da Jarumai:

Arnold Schwarzenegger: Muhammad Ali zai ci gaba da yi wa mutane kaimi. Har abada, abin koyina ne. Kuma ba zai taba gushewa a matsayin wanda ya fi kowa ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jarumin fina-finan Amurka, Arnold Schwarzenegger

Oprah Winfrey: Duniya ta yi rashin gwarzo kuma jarumi. Allah ya jikan ka.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Oprah Winfrey, shahararriyar mai gabatar da shirin talbijin na Oprah, a Amurka.

Madonna: Wannan mutumin. Wannan sarkin. Wannnan jarumin. Wannan dan adam din ! Babu kalmomin da za su bayyana shi. Ya girgiza duniya. Allah yayi masa albarka.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shararriyar mawakiya ta Amurka, Madonna.

Lewis Hamilto: Na matukar girgiza! Allah ya kyautata makomarka zakaran duniya. Allah ya albarkaci iyalansa ya kuma ba su jumurin rashin mahaifin nasu.

Cathy Freeman: Muhammad Ali, alama ce ta daukaka a duniya. Sunansa da bajimtar da ya nuna ba za su gushe ba a duniya. Allah ya jikan ka.

David Becham: Jarumin da ba a taba irinsa ba. Wanda ya fi kowa. Allah ya kyautata makoma.

Pele: Muhammad Ali ya kasance abin koyi har abada.

Anthony Joshua: Ya zama abin koyi kuma zai cigaba da kasancewa a nan gaba.

Lenox Lewis: Daya tamkar da goma, Ali ya nuna hazaka da bajinta a duniya. Allah ya kyautata makwanci.

Amir Khan: Allah ya jikan ka jarumin jarumai.

Mike Tyson: Allah ya karbi ran gwarzo. Allah ya jikan ka.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fitaccen dan damben Amurka, Mike Tyson.

George Foreman: An yi ba za a kara ba. Allah ya jikan ka Muhammad Ali.