Vardy zai yanke shawara kan komawa Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamie Vardy ya taimakawa Kulub din wajen daukar kofin Premier a kakar wasan da ta wuce

A ranar Lintini ne ake sa ran dan wansan Leicester City, Jamie Vardy zai yanke shawara kan ko zai koma Arsenal.

Dan wasan na cikin tawagar Ingila da a ranar ta Litinin, za su tafi Faransa domin buga wasan Euro 2016.

Arsenal da Leicester sun amince cewa, Vardy zai sanya hannu a kontiragin shekara hudu a Arsenal kuma za a bashi albashi mai tsoka.

Rahotanni dai sun ce Leicester na shirin kara albashi ga dan wasan mai shekara 29, wanda ya saka hannu a sabon kontiragin shekara 3 ga kulu din a watan Fabrairu.

Vardy dai ya koma kulub din Leicester ne daga kulub din Fleetown a kan £1m a shekarar 2012 kuma ya taimakawa Kulub din wajen daukar kofin Premier a kakar wasan da ta wuce inda ya ci kwalo 24.