Carneiro ta sasanta da Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A baya Carneiro ta bukaci Chelsea ta dawo da ita kan aiki da albashin kashi 40 cikin dari

Tsohuwar likitar Chelsea, Eva Carneiro ta sasanta da kungiyar a cikin sirri kan sallamarta da aka yi daga aiki.

Carneiro ta yi zargin cewar an yi makarkashiyar sallamarta daga aiki ne, sannan ta yi karar koci Jose Mourinho kan cin zarafi.

A ranar Litinin ne Carneiro ta ki karbar tayin kudi fam miliyan daya da dubu dari biyu, domin su shirya a tsakaninsu.

Tsohon kociyan Chelsea, Jose Mourinho ne ya zargi Carneiro da rashin iya aiki.