Pele zai yi gwanjon lambobin yabonsa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Pele ya ce zai sadaukar da bangaren kudin ne ga aikin jinkai.

Gwarzon kwallon kafar duniya Pele zai yi gwanjon baki dayan lambobin yabo da kyautukan da ya samu a rayuwarsa ta taka tamaula cikin tsawon shekara 60.

A ranar Talata ne ake fara gwanjon kayan a London, kuma ana sa ran za su kai miliyoyin daloli, har kwararru na cewa watakila gwanjon ya kasance mafi girma a harkar kwallon kafa a duniya.

Baki dayan lambobin yabon da ya samu wadanda suka shafi gwala-gwalai da dangoginsu na cikin kayan gwanjon.

Gwarzon ya ce zai sadaukar da bangaren kudin ne ga aikin jinkai, sannan zai so ya ga a girke lambobin yabon nasa a gidajen adana kayan tarihi a sassa daban-daban na duniya.

Shekaru sittin bayan ritayarsa daga buga tamaula, amma har yanzu ya fi kowa zura kwallaye a raga.