'Muna son a bai wa Yusuf Super Eagles'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yusuf ya kwashe shekara 15 yana horar da tamaula a wasannin Nigeria

Dan wasan Lazio, Ogenyi Onazi, ya ce 'yan kwallon Nigeria na son a bai wa Salisu Yusuf jan ragamar Super Eagles.

Tawagar ta Super Eagles ba ta da tsayayyen koci tun bayan da Sunday Oliseh ya yi murabus a cikin watan Fabrairu.

A cikin watan Mayu ne Yusuf ya jagoranci Nigeria ta doke Mali da Luxembourg a wasan sada zumunta.

Onazi ya shaidawa BBC cewar Yusuf ya yi abin a yaba masa, kuma za mu yi murna idan aka ba shi aikin horar da Super Eagles.

Yusuf ya horar da El-Kanemi Warriors da Ranchers Bees, ya kuma jagoranci Kano Pillars lashe kofin gasar Nigeria a shekarar 2008.

Nigeria ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a shekara mai zuwa ba.