Watakila Benteke ya bar Liverpool

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cristian Benteke tsohon dan kwallon Aston Villa ne

Christian Benteke ya ce zai iya barin Liverpool idan har Jurgen Klopp ya ci gaba da kin saka shi a wasanni a kakar mai zuwa.

Brendan Rodgers ne ya sayo Benteke daga Aston Villa, sai dai kuma wasanni takwas ya buga tun lokacin da Jurgen Klopp ya karbi ragamar horar da Liverpool a cikin watan Oktoba.

Benteke ya ce tun lokacin da Klopp ya karbi aiki a Anfield ya fuskanci cewar baya cikin 'yan kwallon da kociyan zai dunga amfani da su a wasanni.

Amma sun tattauna da kocin, kuma yana martabashi, zai duba makomarsa a Liverpool idan an kammala gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.

Benteke yana cikin jerin 'yan wasa 23 da za su wakilci Belgium a gasar ta nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci.