An dakatar da Sharapova shekara biyu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Maria Sharapova ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin

Hukumar kwallon tennis ta duniya ta dakatar da Maria Sharapova daga shiga harkokin wasan tsawon shekara biyu.

A cikin watan Maris ne aka dakatar da Sharapova na kwarya-kwarya, bayan da aka same ta da laifin shan kwayar meldonium mai kara kuzari a gasar Austalia Open.

Sharapova ta ce ta fara shan meldonium tun a shekarar 2006, domin maganin ciwon zuciya, kuma a ranar 1 ga watan Janairun 2016 aka saka sunan kwayar a cikin wadanda aka haramta sha.

'Yar wasan ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da tuni ya fara aiki tun daga 26 ga watan Janairun 2016.