Rangers ta ci Pillars daya mai ban haushi

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption Sakamakon wasannin mako na 21 da aka yi ranar Laraba

Enugu Rangers ta ci Kano Pillars daya mai ban haushi a gasar Premier Nigeria wasannin mako na 21 da suka fafata a ranar Laraba.

Pillars din ta ci gida ne ta hannun Adamu Murtala bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Wasu sakamakon wasannin da aka yi Wikki Tourist ma daya mai ban haushi ta doke El-Kanemi a garin Bauchi.

Karawa tsakanin Akwa United da Sunshine Stars kuwa 3-3 suka tashi, yayin da Abia Warriors da Ikorodu United suka buga kunnen doki 1-1.

Sai a ranar Alhamis ne za a yi karon batta tsakanin Enyimba da Rivers United a garin Aba.

Ga dukkanin sakamakon wasannin makon na 21 da aka buga:
  • MFM 2-0 Nasarawa Utd
  • Lobi 3-1 Shooting Stars
  • Akwa Utd 3-3 Sunshine Stars
  • Abia Warriors 1-1 Ikorodu Utd
  • Wikki 1-0 El-Kanemi
  • Wolves 2-2 Heartland
  • Rangers 1-0 Pillars
  • Tornadoes 1-0 Plateau Utd