Tarihin marigayi Stephen Keshi

Image caption Keshi ya horas da 'yan wasan Super Eagles sau uku

An haifi Steven Keshi a shekarar 1962, a garin Azare na jihar Bauchi.

Keshi ya yi fice a fagen taka leda da kuma horas da 'yan wasa, a nahiyar Afirka.

Shi ne mutum na biyu a Afirka, da ya dauki kofin gasar cin kofin nahiyar Afirka, a matsayinsa na dan wasa da kuma a matsayinsa na kociya.

Steven Keshi, wanda dan wasan baya ne, ya buga akasarin wasanninsa a kungiyoyin wasa na kasar Belgium, sannan daga bisani ya je Amurka domin yin nazari kan dabarun horas da 'yan wasa.

Ya buga wa kungiyoyin kwallon kafa kimanin 11 tamaula a duniya sannan ya horas da 'yan wasa a kasashen Afirka ta yamma da suka hada da Togo da Mali da kuma kasarsa Najeriya.

Mista Keshi ya jagorancin tawagar kwallon kafar Najeriya ta lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 1994, kuma a shekarar ne suka kusa kai wa zagayen wasan dab da na kusa da karshe (quater final) a gasar cin kofin duniya.

A shekara ta 2011 marigayin ya zama kociyan Najeriya, inda kuma ya jagorance ta zuwa gasar cin kofin Afrika wanda ta dauka a 2013, kuma ya kai su zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mista Keshi ya jagorancin tawagar kwallon kafar Najeriya ta lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 1994

Ba a sabunta kwantaraginsa ba bayan kammala gasar cin kofin duniya a Brazil, amma ya ci gaba da zama kocin wuncin-gadi sakamakon gazawar kungiyar kwallon kafar kasar ta kai wa wasan karshe na kofin nahiyar Afirka na shekarar 2015.

An kori Keshi daga aikinsa na kocin-rikon-kwarya, ko da ya ke daga bisani an mayar da shi kan mukaminsa sakamakon sa-bakin da shugaban Najeriya na wancan lokacin Goodluck Jonathan ya yi.

A watan Yulin shekarar 2015 ne aka sallame shi daga aiki, kwata-kwata, kuma a shekarar ne matarsa ta mutu sakamakon cutar daji.