Golan Masar na fatan kafa tarihi a tamaula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masar na buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka

Mai tsaron ragar tawagar Masar, Essam El Hadary, na fatan kafa tarihin wanda ya fi yawan shekaru a gasar cin kofin duniya.

Kasar Rasha ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya da za a yi a shekarar 2018.

A lokacin ne El Hadary zai kai shekara 45 da haihuwa, idan Masar ta samu tikitin shiga gasar.

Mai tsaron ragar Colombia, Faryd Mondragon ne ke rike da lamabar dattijon da ya buga gasar kofin duniya yana da shekara 43 a gasar da Brazil ta karbi bakunci a shekarar 2014.

El Hadary ya yi wa Masar wasa na 144 a karawar da ta doke Tanzania 2-0 a cikin watan Yuni.

Hakan kuma ya sa shi ne dattijo na biyu a Afirka da ya buga wa tawagar kasa wasa, bayan Kersley Appou na Mauritius mai shekara 43 da kwanaki 361 a duniya.