Defoe zai ci gaba da zama a Sunderland

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jermain Defoe tsohon dan kwallon Tottenham ne

Jermain Defoe ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara daya, domin ya ci gaba da murza-leda a Sunderland.

Hakan na nufin Defoe zai ci gaba da zama a Sunderland har zuwa karshen kakar wasan shekarar 2019.

Dan wasan mai shekara 33, ya ci kwallaye 15 a gasar Premier da aka kammala, wanda hakan ya sa kungiyar za ta ci gaba da zama a gasar.

Kocinyan Sunderland, Sam Allardyce, ya ce Defoe daya ne daga cikin kwararru a fagen tarihin cin kwallaye a gasar ta Premier.