Daukakar da na samu tamkar mafarki ne — Rashford

Hakkin mallakar hoto REX FEATUES
Image caption Rashford na cikin 'yan wasan da ke tashe

Marcus Rashford ya ce sanya shi cikin tawagar Ingila da za ta buga gasar cin kofin Turai "tamkar mafarki ne" ganin cewa watan sa hudu da fara buga tamaula a Manchester United.

Dan wasan mai shekara 18, ya zura kwallaye takwas a wasa 18 da ya buga wa United.

Ya ce, "A lokacin bikin Kirsimeti, abin da nake kokarin yi shi ne na shiga tawagar 'yan wasan United 'yan kasa da shekara 21. Don haka ba karamin abin alfahari ba ne da na tsinci kaina a nan. Hakan tamkar mafarki ne idan na tuna baya."

A hirar da ya yi da FATV, matashin dan wasan ya kara da cewa: "Ban taba tunanin shiga tawagar Ingila ba saboda tunani na kawai shi ne na buga wa United kwallo domin kuwa akwai wasanni da yawa a gabanmu."