'Yan kwallon da ba su da kulob a badi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan da kungiyoyi suka sallama a gasar Premier

Kolo Toure da Victor Valdes da kuma Emmanuel Adebayor suna daga cikin manyan 'yan wasan da kungiyoyinsu suka ce su nemi sa'a a gaba.

Toure mai shekara 35, ya murza leda a Liverpool shekara uku, ya kuma buga mata wasan karshe a karawar da aka doke ta a kofin Europa League.

Manchester United ta hakura da mai tsaron raga Victor Valdes, da kuma mai buga mata wasan tsakiya Nick Powell.

Shi kuwa Emmanuel Adebayor ya bar Crystal Palace wadda ya kulla yarjejeniya da ita a cikin watan Janairu.

Manchester City ma ta amince da Martin Demichelis wanda ya buga mata tamaula shekara uku, da ya kara gaba.

Tuni Arsenal ta ce Mikel Arteta da Mathieu Flamini da kuma Tomas Rosicky ba sa daga cikin 'yan kwallon da za su buga mata wasanninta na gaba.

Cikin sunayen da Everton ta fitar na 'yan wasan da za su bar kungiyar har da Tony Hibbert da Leon Osman wadanda kowannensu ya yi shekara 15 a Goodison Park.

A Sunderland kuwa Steven Fletcher da Danny Graham da kuma Wes Brown su ne wadanda ba za su wakilci kungiyar a nan gaba ba.

Shi ma mai tsaron ragar Leicester City, Mark Schwarzer, zai gwada sa'a a kakar badi da wata kungiyar, yayin da Stoke City ta yi ban kwana da tsohon dan wasan Najeriya Peter Odemwingie.