Euro2016: France ta ci Romania 2-1

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan France da Romania na gumurzu a filin Stade de France

Kasar Faransa ta jefa kwallaye biyu a ragar Romania,a wasan bude gasar kwallon kafa ta nahiyar turai wato Euro 2016, da aka buga da daren jiya, a birnin Paris.

Dan wasan Faransar, Olivier Giroud ne ya fara mannawa Romania kwallon farko, bayan da ya sa kai ya hambari kwallon.

Dimitri Payet ne kuma ya jefa kwallon da ta ba wa mai masaukin bakin nasara, a kan Romania.

Sai dai kuma dan wasan Romania, Bogdan Stancu ya ramawa kasar tasa.