Wales ta fara gasar Turai da kafar dama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wales za ta buga da Ingila a ranar Alhamis

Tawagar kwallon kafa ta Wales ta doke ta Slovakia da ci 2-1 a gasar cin kofin nahiyar Turai da suka kara a Faransa a ranar Asabar.

Gareth Bale ne ya fara ci wa Wales kwallon farko a bugun tazara tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Slovakia ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Ondrej Duda.

Haka kuma Wales ta kara cin kwallo na biyu ta hannun Hal Robson-Kanu, wanda ya shiga karawar daga baya.

A ranar Alhamis Wales za ta fafata ne da Ingila a wasa na biyu na cikin rukuni na biyu.