Murray ya sake dawo da kocinsa Lendl

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Murray ya raba gari da Amelie Mauresmo kafin fara gasar French Open

Andy Murray ya sake dauko tsohon kociyansa Ivan Lendl, domin ya ci gaba da horar da shi kwallon tennis.

Rabon da Murray ya yi aiki da koci tun a watan da ya gabata, bayan da ya raba gari da Amelie Mauresmo kafin fara gasar French Open.

Murray ya lashe kofin gasar Wimbledon da na US Open da zinare a gasar Olympic daga tsakanin shekarar 2012 zuwa 2014.

Ivan Lendl zai ci gaba da horar da Murray wasan kwallon tennis da taimakon Jamie Delgado.