Jamus ta samu maki uku a kan Ukraine

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jamus za ta buga wasanta na gaba da Poland a ranar Alhamis

Tawagar kwallon kafa ta Jamus ta doke ta Ukraine da ci biyu babu ko daya a gasar cin kofin nahiyar Turai da suka fafata a ranar Lahadi.

Jamus mai rike da kofin duniya wadda ke harin lashe kofin nahiyar Turai na hudu ta ci kwallayenta ta hannun Shkodran Mustafi da Bastian Schweinsteiger.

Da wannan sakamakon Jamus tana mataki na daya a rukuni na uku, yayin da Poland wadda ta ci Netherland daya mai ban haushi ke matsayi na uku.

Sai a ranar Alhamis ne Ukraine za ta kara da Ireland ta Arewa da kuma wasan da Jamus za ta fafata da Poland.