Matar Vardy ta sha hayaki mai sa hawaye

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ingila za ta kara da Wales wadda ta doke Slovakia 2-1

Uwar gidan Jamie Vardy dan kwallon Leicester City, ta ce ta sha borkonon tsohuwa tun kafin karawar da Ingila ta yi da Rasha a gasar Turai.

Rabekah Vardy ta rubuta a shafinta na sada zumunta na Twitter cewar ta shaki hayaki, aka kuma killace su tun kafin Ingila ta fafata da Rasha a Marseille ranar Asabar.

Tun kafin tawagar Ingila da ta Rasha su fara wasa aka yi taho mugama tsakanin magoya bayan kasashen, daga baya ne kuma mabiya Rasha suka far ma na Ingila.

Rabekah ta ce, ta firgita da hayaniyar ta ritsa da ita, da kuma yadda magoya baya suka yi wa junansu abin firgici ne.

Tuni hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, ta gargadi Ingila da Rasha cewa za su iya fuskantar kora daga buga gasar, idan aka sake samun hatsaniya daga magoya bayansu.