Hamilton ya sadaukar da nasara ga Ali

Lewis Hamilton Hakkin mallakar hoto LEWIS HAMILTON l TWITTER
Image caption Hamilton ya wallafa hotonsa da na Ali lokacin da aka sanar da rasuwar marigayin

Lewis Hamilton ya sadaukar da nasarar da ya samu a gasar tseren motoci ta Canadian Grand Prix ga marigayi Muhammad Ali, wanda ya mutu a kwanakin baya.

Dan tseren na Birtaniya ya rinka maimaita wasu shahararrun kalaman Ali a daidai lokacin da ya ke daf da kaiwa zagayen karshe na gasar.

Ya kara da cewa: "Ali ya karfafa min gwiwa sosai. A don haka zan sadaukar da wannan nasar a gare shi da kuma iyalansa".

A yanzu Hamilton ne na biyu a jeren teburin tseren, inda ya ke bin bayan abokin wasansa na Mercedes Nico Rosberg da maki tara.

Rosberg ya kare ne a mataki na biyar a gasar ta Canada.