Italiya ta doke Belgium da ci 2-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Italiya ta samu maki uku da kwallaye biyu a kan Belgium

Tawagar kwallon kafa ta Italiya ta doke ta Belgium da ci biyu da babu ko daya a gasar cin kofin nahiyar Turai da suka kara a ranar Litinin.

Italiya ta fara cin kwallo ne ta hannun Emanuele Giaccherini bayan da ya samu tamaula daga bugun da Leonardo Bonucci ya yi yo masa.

Dan wasan Southampton, Graziano Pelle ne ya ci wa Italiya kwallo na biyu daf da alkalin wasa zai tashi karawar.

Belgium ta samu damar-makin cin kwallo ta hannun Romelu Lukaku da Divock Origi a karo da dama a wasan.

Italy za ta buga wasanta na gaba da Sweden a ranar Juma'a, yayin da Belgium za ta fafata da Jamhuriyar Ireland a ranar Asabar.