Real Madrid na da kofuna 81 a tarihi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Real Madrid ce ta dauki kofin zakarun Turai na bana kuma na 11 jumulla

Real Madrid tana da kofuna guda 81 da ta lashe tun lokacin da aka kafa kungiyar a ranar 6 ga watan Maris din shekarar 1902.

Madrid din ta fara daukar Copa del Rey a shekarar 1905, bayan da ta ci Athletic Bilbao a wasan karshe, jumulla tana da kofin guda 19.

A shekarar 1929 aka fara gasar league ta Spaniya, kuma sai a kakar wasan 1931-32 ne kungiyar ta fara daukar kofin da a yanzu ake kiransa da La Liga, wanda jumulla ta dauki 32.

Bayan da ta ci kofuna 32 na La Liga da 19 na Copa Del Rey, Madrid ta lashe kofuna 62 a Spaniya ciki har da Supercopa de Espana guda tara da Copa Eva Duarte guda daya da kuma Copa de la Liga.

Real Madrid ce ta fi kowacce kungiya daukar kofin zakarun Turai, inda ta dauki na 11 a bana, bayan da ta ci Atletico Madrid a bugun fenariti, ta kuma fara cin kofin ne a shekar 1955-56.

A dai nahiyar Turai Real Madrid ta lashe UEFA Cup da kuma UEFA Super Cup sau biyu-biyu, jumulla a Turai ta ci kofuna 15.

A wasannin zakarun kungiyoyin kwallon kafa na duniya kuwa, ta dauki Intercontinental Cup a shekarar 1960 da 1998 da kuma 2002.

Haka kuma kungiyar ta dauki FIFA Club World Cup guda daya tilo, wanda ta ci a shekarar 2014.