Portugal da Iceland sun tashi 1-1

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Portugal za ta kara da Austria a wasan zagaye na gaba

Tawagar kwallon kafa ta Portugal da ta Iceland sun tashi kunnen doki 1-1 a gasar cin kofin nahiyar Turai da suka kara a ranar Talata.

Portugal ce ta fara cin kwallo ta hannun Nani saura minti 14 a je hutun rabin lokaci.

Iceland ta farke kwallo ta hannun Birkir Bjarnason minti biyar da dawowa daga hutu.

Sai a ranar Asabar Iceland za ta fafata da Hungary da kuma karawa tsakanin Portugal da Austria.