Everton ta nada Koeman a matsayin kociyanta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shekara biyu Koeman ya jagoramnci Southampton

Everton ta dauko mai horar da 'yan wasan Southampton Ronald Koeman kan yarjejeniyar shekara uku.

Everton za ta biya Koeman kudin diyya da za su kusan kai fan miliyan biyar ga kociyan wanda ya yi aiki da Southampton na tsawon shekara biyu.

Kociyan zai maye gurbin Roberto Martinez wanda Everton ta kora a karshen kakar wasan Premier da aka kammala.

Koeman ya jagoranci Southampton wasanni 76, inda ya lashe guda 36, ya yi canjaras a karawa 15 aka doke shi sau 25, sau uku ya lashe kyautar kocin da yafi fice a Premier na wata-wata.