Juventus ta dauki Miralem Pjanic

Hakkin mallakar hoto Juventus
Image caption Juventus ce ta lashe kofin Serie A da aka kammala na bana

Juventus ta dauki Miralem Pjanic daga Roma kan kudi fam miliyan 25 da dubu dari hudu kan yarjejeniyar shekara biyar.

Tun farko an danganta dan wasan da cewar zai koma Manchester United ko kuma Chelsea da murza-leda.

Pjanic ya koma Roma buga tamaula daga Lyon a shekarar 2011, tuni kuma likitocin Juventus suka tabbatar da ingancin lafiyarsa.

Dan wasan ya ci kwallaye 10 ya kuma bayar da 12 aka zura a raga a wasanni 33 da ya buga a gasar Serie A ta Italiya.