Ronaldo 'ba ya karbar kaddara'

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Ronaldo ya ce Iceland ba ta da wani buri a gasar ta nahiyar Turai

An danganta Cristiano Ronaldo da wanda baya karbar kaddara, bayan da ya soki Iceland kan tashi kunnen doki da suka yi a gasar Turai.

Ronaldo ya cac-caki tawagar Iceland da rashin buri da karancin tunani a fafatawar da suka yi a gasar Euro 2016 da Faransa ke karbar bakunci.

Sai dai kuma dan wasan tawagar Iceland, Kari Arnason, ya mayar wa da Ronaldo martani da cewar ba ya karbar kaddara.

Dan kwallon ya ce suna cikin tsiburi, amma sun buga kunnen doki da tawagar Portugal.

Shi ma tsohon dan kwallon tawagar Iceland, Hermann Hreidarsson ya ce kamata ya yi Ronaldo ya zage damtse ya taimaki kasarsa a wasan da aka yi a Saint-Etienne.