Ko kun san Golan da ya fi cin kwallaye ?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Asmir lokacin da ya ci Southampton ya kuma kafa tarihi

Aikin masu tsaron raga a wasan kwallon kafa ya hada da hana kwallo ta shiga raga.

Sai dai kuma a tarihin kwallon kafa an samu wasu masu tsaron raga da suka kware wajen zura kwallaye a ragar abokan karawarsu.

Ko da ya ke masu tsaron ragar sukan ci abokan wasansu ne a bugun tazara da fenariti.

Tsohon golan Brazil Rogério Ceni shi ne ke kan gaba a matsayin wanda yafi cin kwallaye a raga, inda ya ci 131.

Tsohon dan wasan Sao Paulo ya ci kwallonsa na 100 a ranar 27 ga watan Maris din shekarar 2011.

A cikin watan Nuwambar shekarar 1999, mai tsaron ragar Paraguay, José Luis Chilavert, ya kafa tarihin cin kwallaye uku a wasa.

Golan ya ci kwallaye ukun ne a bugun fenariti a karawar da Vélez Sársfield ta ci Ferro Carril Oeste 6-1.

A kuma ranar 2 ga watan Nuwambar shekarar 2013, mai tsaron ragar Stoke City, Asmir Begovi? ya ci kwallon da mai tsaron raga ya zura a raga a karanci lokacin da aka fara wasa.

Ya ci kwallon ne a ragar Southampton cikin dakika 12 daga yadi 100.