'Zan dawo da martabar Super Eagles'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yusuf ya ce ya san ciki da bai kan horar da Super Eagles

Kociyan riko na tawagar kwallon kafa ta Super Eagles, Salisu Yusuf, ya ce zai dawo da martabar Nigeria a fagen taka-leda a duniya.

A cikin watan jiya ne kociyan ya jagoranci Super Eagles ta doke Mali da Luxemburg a wasannin sada zumunta da suka yi.

Yusuf ya ce lokaci ya yi da ya kamata a ba shi aikin horar da Super Eagles na din-din-din domin ya na da kwarewar da zai kai tawagar ga samun nasara.

Tsohon kociyan El-Kanemi ya ce ya yi aikin mataimakin Super Eagles har karo hudu, wanda hakan ne ya ba shi damar sanin makamar aikin.

Tuni wasu 'yan wasan Super Eagles suka fara kiraye-kirayen cewar ya kamata a bai wa Yusuf aikin horar da tawagar Nigeria.