Ibrahimovic zai taka-leda a Olympic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ibrahimovic yana buga wa tawagar kwallon kafar Sweden gasar nahiyar Turai

Kyaftin din Sweden, Zlatan Ibrahimovic yana cikin 'yan wasa 25 na kwarya-kwarya da za su buga gasar kwallon kafa ta Olympic.

Ibrahimovic mai shekara 34, wanda ke buga wa tawagar Sweden gasar kofin nahiyar Turai, ya ce zai sanar da makomarsa idan an kammala wasannin Faransa.

Kocin Sweden, Hakan Ericson ya ce ya na son ya bai wa Ibrahimovic damar buga gasar, amma zabi ya rage wa dan kwallon.

Ana ta rade-radin cewar da zarar an kammala gasar cin kofin nahiyar Turai, Ibrahimovic zai koma taka-leda a Manchester United.

A karshen kakar bana ne yarjejeniyar Ibrahimovic ta kare da kungiyar Paris St-Germain.