West Ham ta sayi Feghouli daga Valencia

Sofiane Feghouli Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sofiane Feghouli ya halarci gasar cin kofin duniya a Brazil

West Ham ta sayi dan wasan kasar Algeria Sofiane Feghouli daga Valencia kan jarjeniyar shekaru uku.

Sai dai a ba'a bayyana kudin da aka sayi dan kwallon ba.

Dan wasan mai shekaru 26 ya shafe kakar wasanni shida a Spaniya, inda ya zira kwallaye 42 a wasanni 243.

Feghouli, wanda ya lashe kyautar dan kwallon Algeria da ya fi kowanne a 2012, ya murzawa kasar tamaula sau 40.

Hakazalika ya halarci manyan wasanni na kasa-da-kasa sau uku ciki har da gasar cin kofin duniya a 2014.