Euro 2016: Za a hukunta Croatia da Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana ta yin taho-mu-gama tsakanin magoya bayan kasashe daban-daban a wajen Euro 2016

Hukumar kwallon kafar Turai ta kaddamar da kwamitin da zai ladabtar da kasashen Croatia da Turkiyya sakamakon hatsaniyar da magoya bayansu suka tayar a wajen gasar cin kofin Turai ta 2016 da ake yi a Faransa.

Ana zargin magoya bayan Croatia da yin jifa da kuma kalaman da ke nuna wariyar launin fata bayan wasan suka tashi da ci 2-2 tsakaninta da Jamhuriyar Czech ranar Juma'a.

Su ma magoya bayan Turkiyya ana zargin su da yin jefe-jefe da kuma mamaye filin wasa lokacin karawar Spain ta doke su da ci 3-0.