Sundowns ta ci Setif a kofin zakarun Afirka

Hakkin mallakar hoto callo getty
Image caption Sundowns ta kasar Afirka ta Kudu ta samu nasara a wasan farko da ta yi a Algeria

Mamelodi Sundowns ta fara gasar cin kofin zakarun Afirka da kafar dama, bayan da ta ci Entente Setif a Algeria ranar Asabar.

Kungiyoyin sun fara wasan rukuni na biyu na gasar, wanda ya bai wa Sundowns damar cin kwallayenta ta hannun Tiyani Mabunda da kuma Khama Billiat.

Sai dai kuma daf da alkalin wasa zai tashi daga karawar sai magoya bayan Setif suka dunga yin ruwan duwatsu cikin fili.

Hakan ya sa Alkalin wasa ya hura tashi, kuma Setif za ta jira hukuncin da hukumar kwallon kafa ta Afirka za ta yanke kan tada hatsaniyar a lokacin wasa.