Vardy zai watsa wa Arsenal kasa a ido

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Vardy zai ci gaba da taka-leda a Leicester City wadda ta lashe kofin Premier da aka kammala

Jamie Vardy, na daf da shaidawa Arsenal cewar zai ci gaba da murza-leda kungiyarsa ta Leicester City.

Vardy mai shekara 29, bai yanke shawara ba, amma ana hangen cewar zai sabunta yarjejeniyar zama a Leicester City.

An ruwaito cewar Arsenal na son sayen Vardy kan kudi fan miliyan 20, za kuma ta dunga biyansa fan 120,000 a duk mako.

Jin haka Leicester City ta yi wa Vardy tayin cewar za ta biya shi fan 100,000 a duk mako.

Arsenal ba ta da shirin kara kudin da ta taya Vardy, tuni ma ta fara neman wani dan wasan da zai maye mada-dinsa.

Vardy ya koma Leicester daga kungiyar Fleetwood Town kan kudi fan miliyan daya a shekarar 2012.

Arsenal ta bukaci Vardy ya ba ta amsa idan zai taka mata leda, yayin da dan kwallon ya bukaci a ba shi lokaci zuwa bayan gasar cin kofin nahiyar Turai.