Davis ya tsawaita zamansa a Southampton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Steven Davis yana buga wa Ireland ta Arewa gasar cin kofin nahiyar Turai

Dan kwallon tawagar Ireland ta Arewa, Steven Davis, ya sabunta yarjejeniya da Southampton zuwa karshen kakar 2019.

Davis mai shekara 31, wanda ya yi wa Ireland ta Arewa wasanni 81, ya koma Southampton da murza-leda a shekarar 2012 daga Rangers.

Dan wasan ya buga wa Southampton wasanni 155, ya kuma ci kwallaye 11 daga ciki har da guda biyar da ya ci a Premier da aka kammala.

A cikin watanni shida da suka wuce mai tsaron ragar kungiyar Fraser Forster, da James Ward-Prowse da Virgil van Dijk suka sabunta yarjejeniyarsu.