Cavaliers sun lashe gasar NBA

LeBron James Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption James ya taka rawar gani sosai wurin wannan nasarar

Cleveland Cavaliers sun lashe gasar Lig ta cin kofin kwallon kwando ta NBA bayan da suka doke Golden State Warriors.

LeBron James ne ya jagoranci kungiyar wajen samun wannan gagarumar nasara wacce ita ce irinta ta farko a tarihi.

Cavaliers sun lashe wasan karshe 93-89 abin da ya basu nasara kan masu rike da kanbun gasar, wadanda suka lashe wasanni a 73 cikin 82 a kakar NBA ta bana.

James ya samu maki 27 a wasan, sannan ya taimaka a samu 11, abin da ya baiwa Cleveland ndamar lashe gasar a karon farko.

Ya ce "Na bayar da dukkan gudummawar da zan iya".

Shugaba Barack Obama, wanda ya kalli wasan a jirgin Air Force One, ya taya su murnar nasarar da suka samu ta shafinsa na Twitter.