Za a gyara filin tennis na Eastbourne

Hukumar kwallon tennis ta sanar da cewar za a yi aikin gyaran filin Eastbourne kan kudi fan miliyan 44.

Aikin da za a yi shi na tsawon shekara uku zai zama hadaka ce tsakanin Eastbourne Borough Council da Devonshire Park.

Cikin aikin da za a yi har da gina sabbin wajen yin atisaye da dakunan sauya kayan 'yan wasa da wararen ajiyar magunguna da duba marasa lafiya.

Haka kuma hukumar ta sanar da cewar za ta ci gaba da gudanar da gasar ta Aegon International nan da shekara 10 masu zuwa.

Andy Murray ne ya lashe gasar bana kuma karo biyar yana cin gasar, shi ne a matsayin wanda ya fi yawan lashe kyautar.