An kama kocin guje-guje Aden a Spaniya

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption An kai samame ne a otal din da kociyan yake a Spaniya

An kama kociyan Somalia, Jama Aden, mai horas da 'yan wasannin Olympics a Sipaniya.

An gudanar ayyukan hadin gwiwa na tantance masu amfani da kwayoyin kara kuzari ne, tsakanin 'yan sandan Catalan da kungiyar da ke sa ido kan wasannin duniya da kuma hukumar sa ido kan amfani da kwayoyin kara kuzari na Sipaniya.

Mista Aden na horas da 'yar tseren Habasha Genzebe Dibaba wanda ita ce gwarzuwar 'yan tseren mita 500 ta duniya da kuma wasu da ake ganin za su yi fice a gasar wasannin Olympics din bana a Rio.

Babu wanda ya maida martani game da batun, tsakanin Mista Aden ko 'yan wasannin nasa.