Togo ta buga tamaular karrama Keshi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Togo ta je gasar cin kofin duniya a shekarar 2006

Togo ta yi wasan sada zumunta na tunawa da Stephen Keshi, a ranar Lahadi wanda ya mutu a cikin watan Juni.

Keshi wanda ya rasu yana da shekara 54, ya horar da tawagar kwallon kafar Togo sau uku a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2011.

Ya kuma samarwa kasar gurbi a gasar cin kofin duniya a shekara ta 2006 a Jamus.

An buga wasan ne a Lome tsakanin tawagar kwallon kafa ta Togo ta yanzu da kuma ta 'yan wasan da suka murza-leda karkashin Keshi.

Sama da 'yan kallo 20,000 ne suka kalli karawar da tawagar Togo ta yanzu ta doke ta 'yan wasan Keshi da ci 6-2.

Za a dade ana tuna Keshi a matsayin dan kwallon da ya daukarwa Nigeria kofin Afirka ya kuma jagorance ta lashe shi a matsayin mai horarwa.