An karrama 'yan wasan Albania

'Yan wasan Albania Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Albania sun bayar da mamaki kan nasarar da suka samu

Albania ta baiwa dukkan 'yan tawagar kwallon kasar fasfo din alfarma saboda sun doke Romania da ci 1-0 a gasar Euro 2016.

Kasar ba ta taba murza-leda a wata gasar kasa da kasa ba.

Sai dai babu tabbas ko za su samu kaiwa zagaye na biyu na gasar.

Gwamnati ta ce a baiwa tawagar karin kudi Yuro miliyan guda da kuma sabbin fasfo.

Albania sun sha kaye a sauran wasanni biyun da suka fafata, inda suka zo na uku a rukunin.

Fira Ministan kasar Edi Rama ya wallafa "Goooooooooool...." a shafinsa na Twitter lokacin da Armando Sadiku ya zura kwallon da ta ba su nasara a kan Romania.