Binciken kwa-kwaf kan 'yan wasan Rasha da Kenya

Hakkin mallakar hoto IOC

Za a yi binciken kwa-kwaf ga 'yan wasan Rasha da Kenya kafin a basu damar fafata wa a gasar wasannin Olympic ta bana .

'Yan wasan da suka fito daga kasashen da ake ganin ba sa "mayar da hankali" wurin yaki da kwayoyin da ke kara kuzari, na bukatar samun tabbaci na musamman daga hukumomin wasannin da suke yi.

Hukumar wasanni ta Olympic IOC ta tattauna a Lausanne ranar Talata domin amincewa da ka'idoji biyar na yaki da shan kwayoyi masu kara kuzari.

Ta ce "akwai shakku matuka kan batun cewar akwai 'yan wasa masu tsarki daga wadannan kasashe".

IOC ta kara da cewa rashin amintattun kayan yaki da amfani da kwayoyi ya sa ta nemi hukumomin da ke lura da wasanni daban daban su tantance 'yan wasansu.

Sannan ta nemi da su dauki kairn dukkan matakan da suka dace baya ga sharuddan da hukumomin kasashe suke amfani da su.