Spain za ta kara da Italia a wasan zagaye na biyu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Spain za ta fafata da Italia a wasan zagaye na biyu

Croatia ta samu nasara a kan Spain mai rike da kofin nahiyar Turai da ci 2-1 a gasar cin kofin nahiyar da suka kara a ranar Talata.

Spain ce ta fara cin kwallo ta hannun Alvaro Morata, yayin da Nikola Kalinic ya farke wa Croatia, kuma Ivan Perisic ya ci mata ta biyu daf da za a tashi daga wasan.

Da wannan sakamakon Croatia ce ta jagoranci rukuni na hudu, za kuma ta kara a Lens a ranar Asabar, yayin da Spain wadda ta yi ta biyu a rukunin za ta kara da Italia a ranar Litinin.

A wasa na biyu kuwa Turkiya ce ta ci Jamhuriyar Czech da ci 2-0.